Rundunar ƴan sandan ƙasa ta kama yan fashin daji 15

0
19

Rundunar ƴan sandan ƙasa ta sanar da cewa ta kama wasu mutane 15 da take zargin su da aikata laifin fashin daji da garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan.

Mai magana da yawun rundunar Olumiyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar daya fitar, yana mai cewa jami’an tsaron sun kwato makamai a wajen waɗanda ake zargin.

Sanarwar tace jami’an ta dake ƙarƙashin rundunar STS, tare da tallafin mafarauta da yan sa kai sun samu nasarar kamo yan fashin daji 4 a jihar Taraba a watan Afrilu tare da samun nasarar kwato bindigu 3.

A jihar Kaduna kuma, a wani samame da dakaru suka kai ya yi sanadiyyar kama mutum biyar da zargin aikata fashi. An kama ɗauke da bindigogi ƙirar AK-49 da AK-47 huɗu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here