Murƙushe PDP hatsari ne ga siyasar Najeriya—Sule Lamido

0
31

Ɗaya daga cikin manya a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP Sule Lamido, ya yi gargadin cewa ƙoƙarin rusa jam’iyyar su tamkar yunƙurin murƙushe dimokaradiyya ne.

Sule Lamido wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa ne kuma tsohon ministan harkokin waje, ya ce ficewar wasu jiga-jigan PDP zuwa APC mai mulki tuggu ne da ba zai yi wa ‘yan siyasa daɗi ba nan gaba.

Yace kamata yayi Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi adalci, ya san cewa shi shugaban kowa da kowa ne, ya ƙyale yan ‘yan siyasa su yi kokawa da APC a jam’iyyance, inda yace idan Tinubu bai yi hankali ba dabarar za ta ci shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here