Mayaƙan Boko Haram sun kashe mafarauta 10 a Adamawa

0
26

Akalla mafarauta 10 ne suka mutu sakamakon wani harin kwantan ɓauna da mayaƙan Boko Haram, suka kai musu a ƙauyen Kopire dake ƙaramar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

An bayar da rahoton cewa mafarautan da aka kashe sun kasance masu aikin ceto, yayin aka hallaka su da harbin bindiga. Ɗaukacin su sun fito daga ƙananun hukumomin Hawul da Biu dake Borno da kuma Garkida dake Adamawa.

Zuwa yanzu ɗaya daga cikin mafarautan da ya tsira da muggan rauni na cigaba da karɓar magani.

Shugaban kungiyar mafarautan Najeriya reshen arewa maso gabas Shawulu Yohanna, ne ya tabbatar da kai harin tare da yin ala wadai.

Ya kuma nemi Gwamnatin tarayya ta tallafawa ya’yan kungiyar da kayan aiki na zamani wanda zai taimaka musu wajen tunkarar yan ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here