Ƙungiyar kiristoci ta ƙasa CAN, reshen karamar hukumar Zaria ta nemi a bawa mambobin ta damar shiga aikin rundunar Hisbah, a jihar Kaduna, don samar da haɗin kai da kawo sauyi a zamantakewar al’umma.
Sakataren kungiyar CAN yankin Zaria Fasto Nuhu Sani, shine ya nemi hakan a wajen taron da hukumar Hisbah ta Kaduna ta shirya a ranar Litinin, inda yace akwai bukatar mabiya addinin Musulunci da krista su riƙa rayuwa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da haɗin kai.
Yace babu wani addini da mabiyan sa basa aikata laifi, don haka akwai bukatar faɗaɗa ɗaukar ma’aikatan Hisbah zuwa sauran addinai ba iya Muslunci kaɗai ba.
Fasto Nuhu Sani, yace wannan kira in akayi amfani da shi zai kawo samun nasara a aikin rundunar Hisbah ta jihar Kaduna.
A nasa jawabin babban kwamandan rundunar Hisbar, Awwal Abubakar, yace sun samu nasarar bankaɗo haramtattun gurare 150 da ake aikata laifuka a Kaduna, ta hanyar haɗin gwuiwa da sauran jami’an tsaro.