Za’a koma rubuta jarabawar NECO da WAEC a Computer—Gwamnatin tarayya

0
36

Gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin dake shirya jarabawar NECO da WAEC su koma gudanar da jarrabawar su ta hanyar yin amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa wato Computer daga yanzu zuwa shekarar 2026.

Ministan ilimi Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan lokacin da yake yin rangadi ga masu rubuta jarrabawar neman gurbin shiga makarantun gaba da Sakandire a Bwari dake birnin tarayya Abuja, inda yakai ziyarar tare da ma’aikatan hukumar JAMB a yau Litinin.

Yace za’a fara gudanar da jarrabawar NECO da WAEC a computer a cikin watan Mayu na shekarar 2026.

Yace in har hukumar JAMB zata iya shirya jarrabawar computer ga ɗalibai sama da miliyan 2 to babu abinda zai hana NECO da WAEC yin irin haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here