Rasha ta sanar da tsagaita wuta a yaƙin ta da Ukraine

0
24

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya sanar da tsagaita wuta ta kwana uku a yaƙin da ƙasarsa ke yi da Ukraine.

Fadar Kremlin ta ce tsagaita wutar za ta yi aiki daga safiyar 8 zuwa 11 ga watan Mayu, wadda ta yi daidai da ranar tunawa da kawo ƙarshen Yaƙin Duniya na Biyu.

A cewar wata sanarwa, shugaba Putin ya ɗauki matakin ne tsagaita wutar saboda jin ƙai.

Sanarwar tace Rasha tana fatan itama Ukraine zata amince da tsagaita wutar.

Sai dai sanarwar tace idan Ukraine ta karya tsagaita wutar, rundunar sojin Rasha za ta mayar da martani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here