Ranar Talata ce ɗaya ga watan Zul-ƙi’ida—Fadar Sarkin Musulmai

0
68

Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ta ce ranar Talata ce 1 ga watan Zulki’ida na shekarar 1446 bayan hijira.

Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jaririn watan Shawwal ba a ranar Lahadi.

A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.

Hakan na nufin yau Litinin 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here