Gwamnatin jihar Kano, ta sha alwashin tallafawa kungiyar ƴan jarida masu wallafa labarai a kafafen yanar gizo (Online).
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Kano, Kwamared Abdullahi Waiya, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da yake yin jawabi a taron rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar daya gudana a sakatariyar kungiyar ƴan jaridu ta kasa reshen jihar Kano.
Waiya, yace tabbas kafafen yada labarai a kafafen yanar gizo suna da tasiri a rayuwar al’umma, kuma suna bayar da gudummawa ga cigaban al’umma. Ya hori sabbin shugabannin ƙungiyar dasu zamo masu kokarin kawo sauyi mai kyau a cikin harkokin yaɗa labarai da kuma ciyar da jihar Kano gaba.
A nasa jawabin Shugaban kwamitin ƙaddamar da kungiyar wato Alhaji Ahmad Aminu, ya hori masu wallafa labarai a kafafen yanar gizo dasu riƙa tantance labarai kafin akai ga bayyanawa a’lumma, don gudun wallafa labarai na karya ko wanda zasu kawo hargitsi a cikin al’umma. Sannan ya yaba wa Gwamnatin Kano a kokarin da ta bijiro da shi na tsaftace yin magana a kafafen yada labarai.
Shi kuwa sabon shugaban kungiyar ƴan jarida masu wallafa labarai a kafafen yanar gizo, Abubakar Dangambo, yayi alƙawarin yin aiki tare da ƴan kungiyar tare da kare martabar su, da kuma kokarin daukaka harkar yaɗa labarai a kafafen yanar gizo.
Sannan yayi alƙawarin bayar da gudummawa don samar da cigaban a’lummar jihar Kano baki ɗaya.
Sauran shugabannin da aka rantsar sun haɗar da Khadijah Aminu, a matsayin mataimakiyar shugaba, sai Isyaku Ahmad, a matsayin Sakatare, Zahara’u Nasir, a matsayin mataimakiyar sakatare, sai Abbas Yusha’u, matsayin ma’ajin kuɗi da Zainab Bello, mataimakiyar ma’ajin kuɗi.
Taron dai ya samu halartar manyan da ƙananun ƴan jarida daga sassan jihar Kano.