Gamayyar kungiyoyin samarin Arewan kasar nan sun yabawa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk bisa nadin da zai wa Hon Nasir Bala Ja’o’ji, memba a Majalisar Zartaswa ta Babbar Kwalejin Ilimi ta Fasaha ta Tarayya ta Potiskum, a jihar Yobe.
A wata wasikar taya murna ga Ja’ojin wadda shugaban shiyya na kungiyar ya sanyawa hannu, Makama Dan Kaduna, bayan wani taron gaggawa da su ka yi a Kaduna, sun yarda da cewar lallai Ja’oji mutum ne da ya ke da kishin matasa tare da tallafawa rayuwarsu wajen samun cigabansu.
Su ka ce, “Wannan nadi da Sarkin Daura zai masa ya kara inganta sahihancin wani binciken jin ra’ayi da kungiyar ta yi ta gano cewar Ja’o’jin ya na daya daga cikin shugabannin matasa su goma (10) da su ka fi shahara da kwarjini a jihohin Arewa.”
Kungiyar ta yaba da ganin yadda jam’iyyar mulki ta APC ta kasa karkashin shugabancin Dr Abdullahi Umar Ganduje CON, ta yabawa Hon Ja’o’ji kan irin hobbasa din da yake yi wajen ganin an gyara rayuwar matasa a kasar nan.
Bayan taya shi murna da kira gare shi da ya ci gaba da jajircewa wajen tallafawa matasa, sun bayyana cewar “Nan ba da jimawa ba za mu saki sakamakon binciken da mu ka yi mu ka gano samari goma (10) wanda ciki har da Hon Nasir Bala Ja’o’ji da su ka yi fice wajen shahara ta tallafawa rayuwar matasa a fadin Arewacin Najeriya. Za mu yi gagarumin bayar da lambobin girma ga wadannan mutane. Daya bayan daya.”
A wasikar gamayyar kungiyoyin sun ce yanzu ne ma su ka kara samun nutsuwa kan sakamakon binciken da su ka yi, har ya gano musu irin shahara da gwagwarmayar Hon Ja’o’ji wajen samar da yanayin jin dadi da walwala ga matasan da Allah Ya horewa Arewacin Kasar nan.
Su ka ce “Samun jajirtattun shugabannin matasa a wannan bangare namu ba karamin alfanu ba ne ga al’ummar mu. Hakan kuma ya na nuna mana cewar lallai akwai kyakkyawan fatan samun ci gaban al’ummar mu gaba daya.”
Sun kuma bayyana cewar sun tura goron gayyata ga yan kungiyoyin nasu a fadin jihohi goma sha tara (19) na Arewacin Kasar nan. Su ka ce ” Za a ga gagarumin taron da nan kusa ba a ga irin sa ba, wajen nadin sabbin mukamai da wannan Masarauta mai albarka ke yi kwanan nan.”