Kotun Kano ta ɗaure wani mutum daya sare bishiya ba bisa ka’ida ba 

0
36

Wata Kotun Majistare da ke zaune a Rijiyar Zaki, Kano, ta yanke wa Alhaji Inuwa Ayuba hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari ko biyan tara, bayan ta same shi da laifin sare bishiyu guda bakwai a kauyen Sarauniya, cikin karamar hukumar Dawakin Tofa.

An shigar da karar ne a kotu bayan wani rahoto da wata tawagar sa-ido daga Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Kano ta samu. Lauyan gwamnati, Barista Bahijja H. Aliyu, ta bayyana cewa tawagar ta yi saurin kama Ayuba tare da tattara shaidun da suka gabatar wa kotu.

Barista Aliyu ta ce ayyukan Ayuba sun sabawa dokokin kare muhalli da gwamnatin jihar Kano ta shimfida, wadanda ke haramta sare bishiyu ba tare da izini ba.

Bayan nazarin shaidu, kotun ta tabbatar da laifin Ayuba, inda ta ba shi zabin biyan tara ko kuma zaman gidan yari na watanni biyu. Bugu da ƙari, kotun ta umarce shi da dasa sabbin i

Bishiyun neem guda 14 a matsayin diyya bisa laifin da ya aikata.

Da ya ke tsokaci kan hukuncin, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru M. Hashim, ya yabawa tawagar sa-ido ta ma’aikatar da kuma bangaren shari’a bisa jajircewarsu wajen kare muhalli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here