Anyi badaƙalar albashin ma’aikatan ƙananun hukumomi ta Naira miliyan 28 a jihar Kano

0
49
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Kano ta bankaɗo yadda ake wawure Naira miliyan 28 a albashin ma’aikatan ƙananun hukumomi.

A iya watan Maris an gano cewa an yi badaƙalar albashin ma’aikatan ƙananun hukumomi da takai ta naira 27,824,395.40.

Albashin ya kasance na ma’aikata 247, da ake kyautata zaton sun yi ritaya ko kuma sun mutu amma har yanzu ba’a dena fitar da albashin su daga asusun gwamnati ba.

Wannan adadi an same shi a watan Maris kaɗai.

Jaridar Punch tace bayanin hakan na cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran ofishin sakataren Gwamnatin Kano, Muhammad Musa, ya fitar a yau asabar.

Sanarwar tace tuni aka bibiyi yadda aka fitar da kuɗaɗen sannan an mayar da su cikin asusun ma’aikatar ƙananun hukumomi.

Har ila yau, gwamnatin Kano tace za’a binciko masu hannu a wawure kudaden tare da ɗaukar matakin hukunta su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here