Gwamnatin tarayya ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar nan kuɗin guzirinsu a hannu maimakon yin amfani da asusun banki.
Wata sanarwa daga ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ta ce shi ne ya nema wa mahajjatan sauƙi daga Babban Bankin Najeriya CBN.
An bayyana damuwa game da tsarin da CBN ya sharɗanta na kowane mahajjaci ya yi amfani da katin banki a matsayin wanda zai iya kawo tarnaƙi ga tsari da aikin gudanar da Hajjin 2025, in ji sanarwar da mai magana da yawun Shettima Stanley Nkwocha ya fitar.