Shan giya ne ke haddasa tashin hankali tsakanin al’umma—Rundunar Hisbah

0
27

Rundunar Hisbah ta jihar Kano, ta ƙara jan hankalin al’umma dasu cigaba da kiyaye dokokin Allah don kaucewa fushin sa.

Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr. Mujahiddin Aminudden, ne ya bayyana hakan lokacin da yake yin jawabi akan yadda Jami’an Hisbah suka samu nasarar kama wata babbar mota maƙare da kwalaben giya da suka zarce dubu 14, wadda darajar kuɗin ta yakai Naira miliyan 30.

Masu shigo da giyar sun yi amfani da taliyar yara wajen yin basaja don kawar da hankalin mahukunta daga kama giyar, inda suka rufe giyar da taliya.

Dr. Mujahiddin Aminudden, yace sun kama direban motar giyar mai suna Emmanuel, inda ake cigaba da gudanar da bincike akan sa.

Rundunar Hisbah, ta kara da cewa yawan ta’ammali da giya ko kayan maye na daga cikin abin da ke haddasa rikice rikice tsakanin al’umma.

Akan haka ne rundunar Hisbah ke neman tallafin al’umma dasu cigaba da bata bayanan sirri a duk wajajen da ake samun aikata laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here