Hukumar gudanarwar jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake jihar Bauchi ta kori ma’aikacin ta mai suna Dr. Usman Aliyu.
Daraktan yaÉ—a labarai na jami’ar Zailani Baffa, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Alhamis a birnin Bauchi.
Yace an É—auki matakin korar malamin bayan samun sa da laifin cin zarafin wata matar aure, yayin zaman majalisar gudanarwar jami’ar daya gudana a ranar 11 ga watan Afrilu.
Daraktan yaÉ—a labaran, ya tabbatar da cewa kwamitin ladabtawar jami’ar ya samu Dr. Usman da aikata abin da ake zargin sa da yi.