Gwamnan riƙon Rivers ya halarci taron majalisar tattalin arzikin ƙasa

0
36

A karon farko Gwamnan riƙon jihar Rivers Ibok Ete Ibas, ya halarci taron majalisar tattalin arzikin ƙasa.

Wannan shine lokacin farko da gwamnan riƙon ya halarci zaman majalisar tattalin arzikin ƙasar tun bayan da shugaban ƙasa Tinubu, ya naɗa shi bayan dakatar da Siminalaya Fubara.

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ne ke jagorantar zaman dake gudana yanzu haka a fadar shugaban ƙasa.

Taron majalisar tattalin arzikin ƙasa dai ya kasance wanda ake tattaunawa akan yanayin tafiyar tattalin arzikin ƙasa tsakanin mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da kuma Gwamnan babban bankin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here