Ganduje ya karɓi Kawu, Baffa Bichi da sauran ƴan jam’iyyar NNPP

0
31

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi Sanatan Kano ta Kudu Abdurrahman Kawu Sumaila, bayan ficewar sa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a yammacin jiya Laraba.

Mai taimakawa Ganduje a fannin sadarwa Aminu Dahiru, ne ya sanar da hakan cikin saƙon daya wallafa a shafin na Facebook.

Bayan Kawu Sumaila, Ganduje ya tattauna da wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP da suka haɗa da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Baffa Bichi da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta Makoda, Hon. Badamasi Ayuba.

Sauran sun hada da Hon. Abdullahi Sani Rogo da Rt. Hon. Zubairu Hamza Masu da Hon. Muhammad Diggol da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da Hon. Abbas Sani Abbas.

Zuwa yanzu dai Kawu Sumaila, ne kaɗai ya bayyana ficewar sa daga NNPP zuwa APC, a tsakanin ƴan majalisar dokokin kasa dake cikin jam’iyyar ta NNPP.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas, ya kasance tare da Ganduje, yayin tattaunawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here