Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta musanta labarin dake cewa ta haramtawa mutane sauraron waƙar Hamisu Breaker mai suna Amana ta, bisa zargin sanya kalaman batsa a cikin ta.
Daily News 24 Hausa, ta rawaito cewa mataimakin babban kwamandan rundunar Dr. Mujahiddin Aminudden, ne ya bayyana hakan, bayan fitar wani labarin dake cewa mataimakiyar babban kwamandan Hisbah bangaren mata Dr. Khadija Sagir, tayi ala wadai da waƙar tare da neman matasa su guji sauraron ta.
Dr. Mujahiddin Aminudden, yace haramta sauraron waƙa ba aikin su bane, inda yace aiki ne na hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jiha.