Babban Sufeton yan sandan ƙasa Kayode Egbetokun, ya shawarci al’ummomin da jami’an tsaro ke aiki a yankunan su da su daina ba su bashi ko aron kuɗi da ƴan sandan zasu gaza biya.
Egbetokun, ya bayyana hakan ta bakin Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kogi, Miller Dantawaye, lokacin daya wakilce shi a wajen bikin ƙaddamar da sabuwar shalkwatar ‘yan sanda a yankin Imane, dake karamar hukumar Olamaboro a jihar ta Kogi.
Yace ina jan kunnen al’ummar wannan yanki cewa yayin da suke mu’amala da jami’an da za a turo musu, wasu daga cikinsu za su nemi taimakon kuɗi da rance, amma kada ku ba su rance mai yawa da za su gagara biya.
Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su kula da sabon ofishin ‘yan sanda, wanda shine irinsa na farko a yankin, wanda wani ɗan asalin yankin, Dr. Peter Ali, ya gina kuma ya bayar kyauta.
Haka kuma, Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, wanda Mataimakinsa, Joel Oyibo, ya wakilta, ya nuna godiyar gwamnatin jihar ga kyautar da aka bayar, sannan ya ƙarfafa al’umma da su haɗa kai da jami’an da za a turo don yin aiki a yankin.