Kamfanin rarraba lantarki na Kano, KEDCO ya ƙaryata labarin cewa wutar lantarki ta awanni 2, kacal ake samu a Kano, Katsina da Jigawa.
Cikin wata sanarwar da kamfanin ya fitar yace abu na gaskiya shine an samu raguwar wutar lantarki da abokan hulɗar sa ke sha da kaso 20 zuwa 30.
Idan za’a iya tunawa a jiya Talata ne aka samu fitar labarin cewa wasu a’lummar jihohin da KEDCO ke rarraba lantarki sun nuna damuwa akan ƙarancin wutar da suke samu, wanda hakan ya haifar da asara ga wasu masu yin ƙananun sana’o’in da suka dogara da lantarki.