Gwamnan jihar Neja Umaru Muhammad Bago, ya sanya dokar hana fita a Minna daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safiya biyo bayan ƙaruwar kashe kashen mutane a ƙwaryar birnin.
Gwamnan yace a tsakanin lokacin da aka saka dokar an haramta yin zirga-zirga da baburan masu haya masu kafa biyu ko uku.
Gwamna Bago, ya bayyana hakan a yau Talata lokacin da ya jagoranci gudanar da wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki a fannin tsaro da masu riƙe masarauta a fadar gwamnatin jihar.
Sai dai yace dokar hana fitar bata shafi masu aikin bayar da kulawar lafiya ba, inda yace an saka dokar da manufar daƙile ayyukan rashin tsaron da jihar Neja ke ciki a halin yanzu.
A yayin taron ya umarci masu unguwanni da dagatai su riƙa kula da baƙi masu shigowa cikin al’umma, sannan yace za’a rushe duk gidan da aka samu suna ɓoye ƴan ta’adda ko masu safarar kayan maye.