Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya amince a fitar da kuɗaɗen da yawan su yakai Naira miliyan 850, da za’a yi amfani dasu wajen gyara rijiyoyin burtsatse a Maiduguri da kewaye.
Yunkurin baya rasa nasaba da kokarin magance matsalolin rashin ruwan sha da ake fama da ita a Maiduguri biyo bayan ambaliyar ruwan da birnin ya fuskanta a ranar 10 ga watan Satumba na shekarar 2024.
Shugaban hukumar samar da ruwan sha a ƙauyukan Borno Dr. Muhammad Musa Aliyu, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin Maiduguri.
Yace gwamna Zulum ya bayar da umurnin fitar da kuɗin don siyo duk wasu abubuwan da za’a yi amfani da su wajen gyara rijiyoyin, a Maiduguri da kewaye.