Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo, ya dakatar da Dr. George Egabor, wanda mai riƙe da sarautar gargajiya ne a ƙaramar hukumar Etsako ta gabas, biyo bayan ƙaruwar ayyukan garkuwa da mutane da kashe kashe a yankin sa.
Dakatarwar ta fito cikin wata sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Edo ya fitar a birnin Benin.
Sanarwar tace an dakatar da Dr. George Egabor, har sai baba ta gani.
Gwamnatin Edo tace kafin yanzu an kama Sakataren masarautar wato Peter Omiogbemhi, biyo bayan faruwar lamarin da yayi sanadiyar mutuwar wani masarauci mai suna John Ikhamate.