Fashewar wasu abubuwa ta kashe mutane a jihar Kaduna

0
33
Kaduna

Fashewar wasu abubuwa tayi sanadiyar mutuwar wasu kananan yara ƴan shekara 13, da 6 a yankin Abakpa, dake jihar Kaduna.

Yaran da suka mutu sune Imam da Nasrin, sai wasu mutane 3 da suka ji munanan rauni, a fashewar data faru a tsohuwar makarantar horas da sojoji ta NDA dake Kaduna a yau Talata.

Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa zuwa yanzu ba’a gano dalilin fashewar ba, duk da cewa jami’an tsaro na wajen da abin ya faru don gudanar da bincike.

Wani mazaunin yankin da abun ya faru ya shaidawa Daily trust, cewa yana tsaka da yin wanka lokacin da yaji fashewar, wanda hakan ya sanya shi tserewa.

Zuwa yanzu dai babu wata sanarwar da hukumomin tsaro suka fitar akan wannan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here