Wani saurayi da budurwar sa sun rasa rayukansu a wani ɗaki da aka tabbatar na saurayin ne a unguwar Alo dake ƙaramar hukumar Ankpa ta jihar Kogi.
An gano gawarwakin a ranar Juma’a da ta gabata, a cikin gidan haya da saurayin ke zaune, bayan da aka gane cewa bai fito daga dakin nasa ba tsawon lokaci.
Mai gidan da saurayin ke yin haya ne ya fara lura da rashin ganin matashin, wanda hakan yasa shi neman taimakon sauran mutane da jami’an yan sanda don buɗe dakin nasa a samu tabbacin me ke faruwa.
Ƴan uwan saurayin da jami’an yan sanda ne suka ɓalle kofar ɗakin inda suka tarar da gawar shi da budurwar tasa kwance akan gado tsirara.
Daga nan an ɗauki gawar tasu zuwa asibitin Ankpa, wanda a nan ne likitoci suka tabbatar da rasuwar matasan.
Zuwa yanzu dai an cigaba da gudanar da bincike don sanin dalilin rasuwar tasu.