An kama mai garkuwa da mutane a jihar Kano

0
40

Dakarun soji sun kama wani mutum ɗan shekaru 55 a lokacin da suke yin sintiri a ƙauyen Sumama dake karamar hukumar Tudun Wada, a jihar Kano, inda ake zargin sa da aikata garkuwa da mutane.

Mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin shiyya ta 3 dake jihar Kano Kaftin Babatunde Zubairu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar daya fitar a yau Talata.

Yace an samu mutamin da ake zargin da manyan makamai a ranar 20 ga watan Afrilu.

Sanarwar tace an gabatar da mutumin ga kwamandan rundunar Birgediya janar Ahmad Tukur, lokacin da yake yin bikin Easter tare da sojoji a sansanin sojoji na Falgore dake ƙaramar hukumar Doguwa. Birgediya Tukur, ya bayyana jin daɗin sa akan namijin ƙoƙarin da sojojin suka yi.

Daga cikin makaman da aka samu tare da mai garkuwar akwai, bindigu, harsashi da sauran manyan makamai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here