Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Najeriya a yau Litinin bayan shafe makonni a Faransa da birnin Landan.
Mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan cikin wani saƙon daya wallafa a shafin sa na X, a ranar Litinin, yana mai cewa Tinubu zai dawo Najeriya a yau.
A ranar 2 ga Afrilu, ne Shugaba Tinubu ya bar Najeriya zuwa birnin Paris, Faransa, don ziyarar aiki.
Onanuga ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa zai yi nazari kan yadda gwamnatinsa ta yi aiki zuwa yanzu da kuma duba manyan nasarori da ya samu.
Sai dai tafiyar tasa ta bar baya da ƙura, bayan da aka riƙa samun hare haren yan bindiga, lamarin da yasa ƴan adawa neman ya dawo gida don tunkarar ƙalubalan da ƙasar ke ciki.