Paparoma Francis, ya mutu yana da shekaru 88 a duniya.
Fadar Vatican ce ta sanar da mutuwar tasa a yau Litinin bayan yasha fama da rashin lafiya.
Paparoma Francis, shine shugaban ɗariƙar Katolika, ta duniya.
Mutuwar tasa tazo a daidai lokacin da mabiya addinin kirista ke shagulgulan bikin Esta a yau Litinin.