Muna goyon bayan samar da hukumar kiwo da makiyaya—Sarkin Kano na 15

0
50

 Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa kafa Hukumar kula da kiwo da makiyaya ta kasa. 

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana haka ne a lokacin da Shugaban Kungiyar Fulani ta Kasa ya kai masa ziyara a fadar sa. 

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran Sarkin Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ya fitar a yau Litinin.

Yace wannan wani babban cigaba ne ga al’ummar Fulani da Makiyaya dama arewacin Najeriya baki ɗaya. 

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kuma godewa Shugaban kasa bisa kafa kwaminti na kula da bangaren makiyaya kuma ya damka kwamitin ga Farfesa Attahiru Jega tare da tsohon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje. 

Ya bukaci shugabannin Kungiyar dasu mayar da hankali da cigaba da jajircewa wajan tabbatar da nasarar taron da zasu gudanar a watan gobe yana mai cewa hakan zai sa a samu hadin kai a tsakanin fulani Makiyaya da sauran al’umma. 

Da yake gabatar da jawabi Shugaban Kungiyar fulani na Kasa Alhaji M.B Lamido yace sun kaiwa Alhaji Aminu Ado Bayero, ziyarar ne domin yi masa barka da Sallah da kuma yi masa ta’aziyyar rasuwar wasu mafarauta “yan asalin jihar Kano da akayi musu kisan gilla a jihar Edo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here