Majalisun dokokin ƙasa sun tsawaita lokacin hutun su

0
32

Majalisun dokokin ƙasa sun tsawaita lokacin hutun su zuwa ranar 6 ga watan Mayu.

Ɗan majalisa Kamoru Ogunlana, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar daya fitar a yau Litinin.

Cikin sanarwar Kamoru Ogunlana, ya sanar da yan majalisun dokokin ƙasa cewa an umarce shi ya sanar da su ƙara wa’adin komawar su aiki daga ranar 29 ga watan Afrilu zuwa 6 ga watan Mayu.

Sanarwar tace ƙarin zai bawa ƴan majalisar damar yin hutun ranar ma’aikata da kuma yin wasu ayyukan a mazaɓun su.

Daga ƙarshe ƴan majalisar sun nemi afuwa ga duk wanda ƙarin lokacin hutun ka’iya haifar wa da rashin jin dadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here