Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce wasu na son yin amfani da rashin zuwan tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari Abuja domin nuna cewa akwai ɓaraka tsakaninsa da shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Gwamna Sule ya bayyana hakan yayin da alamu suka bayyana cewa an samu ɓaraka tsakanin makusantan tsohon shugaban ƙasar, waɗanda suka kasance a jam’iyyar CPC, wadda Buhari ya jagoranta kafin shiga haɗakar da ta samar da jam’iyyar APC.
A baya-bayan nan wani ɓangare na ƴaƴan tsohuwar jam’iyyar ta CPC sun bayyana mubaya’arsu ga shugaba Bola Tinubu, sai dai kwanaki kaɗan bayan hakan wasu ƴaƴan tsohuwar jam’iyyar kuma waɗanda ke da matuƙar kusanci da Buhari suka nesanta kansu daga mubaya’ar.
Haka nan sauya sheƙar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda shi ma makusancin tsohon shugaban ƙasar ne ya ƙara ɗora ayar tambaya kan alaƙar da ke tsakanin tsohon shugaba Muhammadu Buhari da kuma shugaba mai ci Bola Tinubu.
Sai dai a tattaunawarsa da BBC, Abdullahi Sule ya ce maganar cewa abubuwa sun yi lalace duk kuskure ne, don ba ya zuwa Abuja shi ne za a ce ba ya tare da wannan gwamnatin, ina jin wannan kuskure ne.
Haka nan gwamnan ya musanta batun cewa sun ziyarci tsohon shugaban ƙasar da nufin shawo kansa kada ya fice daga jam’iyyar.