Wata ambaliyar ruwa tayi sanadiyar mutuwar mutane 3 a jihar Neja, tare da lalata gonakin shinkafa masu girman Hekta dubu 10, a ƙaramar hukumar Mikawa.
Ana kyautata zaton cewa ambaliyar ruwan tazo bayan buɗe madatsar ruwa ta wutar lantarki dake yankin Jebba.
Rahotanni sun bayyana cewa gonakin shinkafar sun lalace kafin akai ga girbe su, sannan ruwan ya tafi da amfanin gonakin.
Ɗaya daga cikin mutanen da gonakin su suka lalace sanadiyar ambaliyar mai suna Abdulrahman Abdulƙadir, yace gonar sa ta shinkafa mai girman Hekta uku itama ta lalace.
Yace basu san dalilin da yasa aka saki ruwan ba, a daidai lokacin da amfanin gonakin mutane suka kai ga girbi.