Najeriya ta kori ƴan ƙasar Mali da suka shigo ƙasar ba bisa ka’ida ba

0
39

Hukumar shige da fice ta ƙasa ta sanar da mayar da wasu ƴan ƙasar Mali 62 da suka shigo Najeriya ba bisa ƙa’ida ba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa babban jami’in hukumar NIS mai kula da iyakar Najeriya ta Illela Tony Akuneme, yace mutanen sun haɗar da mata maza 51 sai mata 11.

Akuneme ya ce jami’an hukumar ne suka yi wa mutanen rakiya daga shalkwatar hukumar shige da fice ta ƙasa da ke Abuja zuwa kan iyakar Illela da ke jihar Sokoto, cikin motocin bas biyu.

Ya ƙara da cewa bayan tanatance takardunsu, an miƙa su ga jami’an ƴan sandan Nijar da ke Birnin Konni.

A watannin da suka gabata ma Najeriya ta mayar da wasu ƴan ƙasashen Mali da Togo da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here