Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sanya hannu kan takardar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin yin garkuwa da mutane a jihar, kamar yadda doka ta tanada.
Majalisar dokokin jihar Edo ce ta zartar da wani kudiri na gyaran dokar hana satar mutane (da kuma masu alaka da su ta 2013), wacce ta tanadi hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane da kuma tilasta kwace da rushe dukiyoyin da aka yi amfani da su wajen aikata laifukan da su ka aikata.
Gwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a dakin taro na Uromi da ke karamar hukumar Esan Arewa maso Gabas inda ya tattauna da shuwagabanni da ‘yan kungiyar Arewa mazauna kasar Esan.
Don haka ya yi kira ga masu aikata irin wannan laifi da su daina aikata wa.