Ba’a hana ni shiga fadar shugaban ƙasa ba—Kashim Shettima

0
56

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya karyata rahotannin da ke cewa an hana shi shiga fadar shugaban kasa, don gudanar da aiki.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce wadanda ba su san yadda ake gudanar da gwamnatin Najeriya ne kadai zasu yadda da irin wannan labari, wanda hankali ba zai dauka ba.

A jiya Juma’a ne wasu jaridu suka ruwaito cewa, jami’an tsaro sun hana mataimakin shugaban kasar shiga Villa, har sai shugaba Tinubu ya dawo daga kasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here