Za mu karrama Janar Tiani da lambobin yabo saboda zaben harshen Hausa don amfani da shi a hukumance – Ibrahim Abubakar

0
39

Shugaban matasa ‘yan gwangwan mazauna Ogun, Ibrahim Abubakar, wanda dan asalin unguwar Rimin Auzinawa ne a karamar hukumar Ungoggo ta Jihar Kano, ya shirya bayar da lambobin yabo da kyaututtukan girmamawa ga shugaban mulkin sojin jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani.

Ibrahim Abubakar ya ce wannan girmamawa ta musamman ta biyo bayan matakin da Janar Tchiani ya dauka na tabbatar da harshen Hausa a matsayin harshen Jamhuriyar Nijar a hukumance, wani ci gaba da ke kara habaka martabar harshen a matakin duniya.

A cewarsa, ya dauki aniyar mika wadannan lambobin karramawa ga shugaban kasar ta Nijar ne domin nuna godiya da yabo daga al’ummar Hausawa. 

Ya ce yana amfani da kafafen sadarwa na zamani domin isar da wannan sako cikin sauki da tsari, tare da fatan samun hadin kai daga hukumomin jamhuriyar ta Nijar wajen karbar karramawar cikin mutunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here