Sai Kwankwaso ya jingine Kwankwasiyya zamu karɓe shi—Abdullahi Abbas

0
36

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi kira ga jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da kar ya shigo APC da kungiyar siyasar sa mai suna Kwankwasiyya.

Idan za’a iya tunawa an samu raɗe radin cewa Kwankwaso, na shirin sauya sheka zuwa APC.

Sai dai kuma da ya ke jawabi a yayin taron manema labarai a sakatariyar APC ta Kano a yau Juma’a, Abdullahi Abbas ya ce ba ruwan APC da wata ƙungiya ta siyasa a cikin jam’iyyar.

Ya kara da cewa duk masu tururuwar dawowa APC ba za a ki karbar su ba amma sai sun je mazabun su sun yi rijista.

Ya kuma ce dukkanin shugabannin da ke rike shugabancin jam’iyyar a matakai daban-daban a jihar suna nan akan mukaman su babu canji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here