Sanatan Kano ta Kudu Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, yace suna kan tattaunawa da sauran ƴan majalisun tarayya don yanke shawara akan makomar siyasar su.
Kawu Sumaila, ya bayyana hakan a jiya Alhamis bayan wata ganawa da tsohon sakataren gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi, tsohon Kwamishinan sufuri Muhammad Diggol, Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, Abbas Sani Abbas, Kabiru Alhassan Rurum, Abdullahi Sani Rago da sauran su.
Kawu yace bayan mutanen da aka ga fuskokin su yayin ganawar akwai sauran yan siyasa da suke tattaunawa dasu, inda nan gaba kaɗan zasu bayyana matsayin su, da inda zasu karkata.