Wasu ƴan bindiga sun kai hari garin Faruruwa da ke Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu sannan suka yi garkuwa da wasu mutanen.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin a daren ranar Alhamis tare buɗewa wuta.
Wani shaida, Ibrahim Faruruwa, ya ce maharan sun yi yunkurin sace wani hamshakin dan kasuwa, Alhaji Haruna Halilu, sai dai ba ya shagon sa a lokacin harin.
Ya ce da basu samu Alhaji Haruna ba, sai suka sace dansa, Mas’ud.
Ya kara da cewa maharan sun kashe mutane biyu wato Alhaji Rabiu Faruruwa da Sahabi Dankwaro a yayin harbe harben da su ka riƙa yi.
Da Daily Nigerian ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yansandan jihar Kano Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya ce zai bincika lamarin kafin yace komai.