Za’a hukunta ƴan sandan da suka karɓi Kuɗin ƴan China

0
42

Rundunar ƴan sandan ƙasa ta ce za ta ɗauki matakin hukunta wasu jami’anta da aka nuna suna ƙarbar kuɗaɗe daga hannun wasu ƴan ƙasar China a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.

A cikin bidiyon, an ga wasu ƴan ƙasar China suna rabawa wasu jami’an ƴan sanda kuɗi, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, musamman inda ƴan Najeriya da dama ke nuna rashin jin daɗinsu tare da yin kira da a kawo sauyi kan yadda rundunar ke gundanar da ayyukanta.

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar ƴan sandan na X, kakakin rundunar na ƙasa Muyiwa Adejobi, ya yi Allah-wadai da halin jami’an, inda ya bayyana abin da suka yi a matsayin rashin ɗa’a.

Ya ƙara da cewa rundunar ta zuƙulo jami’an da lamarin ya shafa kuma ana shirin ɗaukar matakan ladabtarwa a kansu.

Ko da yake bai bayyana yanayin matakan da za a ɗauka kan ƴansanda ba, Adejobi ya tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here