Babu maganar komawar Kwankwaso cikin jam’iyyar APC—Buba Galadima

0
71

Jigo a tafiyar jam’iyyar NNPP, a matakin kasa Buba Galadima, ya karyata jita-jitar da ake yadawa akan cewa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, yana shirin komawa jam’iyyar APC.

Galadima, wanda daya ne daga cikin na kusa da Kwankwaso ya ce NNPP na bai wa ’yan Najeriya haske kan abin da jam’iyyar za ta iya bayarwa ta hanyar shugabanci nagari da gaskiya, yana mai cewa ’yan siyasar da suka gaza ne kawai ke maganar zaben gaba tun kafin wa’adinsu ya kare.

A baya-bayan nan, ne dai Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen cewa Kwankwaso zai dawo APC.

Galadima yace ko Ganduje kadai ya isa ya hana mutane son shiga APC, yana mai cewa shugaban kasa Tinubu ne kadai zai iya bawa Gandujen damar zama shugaban APC a matakin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here