Gwamna Caleb Mutfwang, na jihar Filato, ya shawarci matasa dasu tashi tsaye domin kare a’lummar yankunan su daga hare haren yan bindiga.
Mutfwang, ya bayyana hakan a ranar talata lokacin da yakai ziyarar ta’aziyyar rasuwar wasu mutane masu yawa da yan ta’adda suka kashe a yankin Kwall dake Æ™aramar hukumar Bassa, lokacin da aka kai musu hari.
Yace a halin da Najeriya ke ciki yanzu haka anzo gaɓar da kowa zai tashi domin kare kansa da yankin sa daga yan bindiga, sai dai yace amma duk da haka baya goyon bayan karya doka.
A daren Lahadin data gabata ne idan za’a tuna wasu mahara suka farmaki a’lummar yankunan Zike, da Kimakpa, dake yankin Kwall ta Æ™aramar hukumar Bassa, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutane 52, tare da Æ™one gidaje da lalata duniyoyi.
Gwamnan na Filato, yace gwamnatin sa tana yin bakin kokari wajen dakile ayyukan ta’addanci, sannan ya nemi Gwamnatin tarayya ta Æ™ara kaimi wajen yaÆ™ar rashin tsaro.