Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙara rage farashin litar man fetur zuwa Naira 835.
An rage farashin man daga tsohon farashin sa na Naira 865, da hakan ya nuna cewa an samu sauƙin kaso 3.5 cikin ɗari.
Wannan ragi ya biyo bayan karyewar farashin ɗanyen man fetur a kasuwannin duniya, wanda kowacce ganga ɗaya ta koma dala 64, daga dala 70 a ƴan kwanakin nan.