Ɗan sanda yaƙi karɓar cin hancin Naira miliyan 1 daga wajen ɓarayin mota a jihar Katsina.
Ɓarayin sun nemi bayar da cin hancin a lokacin da jami’an tsaron suka kama su, su biyu tare da gano mota da sauran abubuwa.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar daya fitar a yau Laraba.
Yace an kama ɓarayin a ranar 11 ga watan Afrilu da misalin karfe 3 na rana a kauyen Birnin Kuka, dake ƙaramar hukumar Mashi, ta jihar Katsina, a lokacin an kama matasa biyu masu kimanin shekaru 26, 27, masu suna Mubarak Kabir da Adamu Hashim mazauna unguwar Kurna dake jihar Kano.
A yayin bincike an gano cewa matasan sun sato motar da suke ciki daga birnin tarayya Abuja, sannan ana zargin su da aikata wasu laifukan a daidai lokacin da ake cigaba gudanar da bincike.
Kwamishinan ƴan sandan Katsina CP Bello Shehu, ya yabawa kokarin jami’an tsaron tare da neman su cigaba da yin abubuwan da zasu ɗaga darajar aikin su.