Yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara tare da yin ajalin mutane da dama

0
141

Wasu da ake kyautata zaton yan bindiga ne sun kai hari garin Morai dake karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.

Mutanen sun kai harin da tsakar daren Litinin wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 4, da kuma sace wasu da dama.

Cikin waɗanda aka kashe akwai tsohon shugaban ƙaramar hukumar mai suna Saminu Morai.

Harin ya tayar da hankalin al’umma sakamakon harbin kan mai uwa da wabi da Æ´an bindigar suka riÆ™a yi.

Tuni dai aka gudanar da jana’izar Mutanen da aka kashe, wanda Sarkin Talata Mafara da jami’an yan sanda suka halarta.

Sai dai kawo lokacin rubuta wannan labari ba’a ji wani Æ™arin bayani daga rundunar Æ´an sandan jihar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here