Tinubu ya nemi a kawo karshen kisan mutane a jihar Filato

0
77
Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana rashin jin daɗin da akan kashe mutane da wasu ƴan bindiga suka yi a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Tinubu ya yi Ala wadai da lamarin, sannan ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar jihar inda ya buƙaci a nemi hanyar warware rikicin da kuma samar da zaman lafiya.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar, inda Tinubu yace akwai bukatar haɗin-kai ba tare da nuna bambacin addini ko kabila.

Shugaban Najeriya Tinubu ya ƙara da cewa dole ne shugabannin al’umma da na addini da kuma siyasa su haɗa-kai don daƙile waɗannan hare-hare da suka addabi jama’a.

Aƙalla mutum 50 ne suka mutu a harin da ƴan bindigar suka kai jihar a cikin daren Litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here