Najeriya ce tafi kowacce ƙasa fitar da ɗanyen man fetur a Afrika—OPEC

0
68

Rahoton Kungiyar Kasashe Masu arzikin Man Fetur ta Duniya (OPEC) ya nuna cewa Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na ƙasa mafi samar da ɗanyen fetur a nahiyar Afirka a watan Maris.

OPEC ta ce hakan ya faru duk da raguwar yawan man da ƙasar ta samar a watan da ya gabata.

OPEC tace yawan man da Nijeriya ta samar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.40 a kowace rana a watan Maris, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 da ta fitar a kowace rana a watan Fabrairu.

A cewar rahoton, duk da raguwar, yawan man da Nijeriya ta samar shi ne mafi yawa a Afirka, inda ya zarce na kasashen Algeria da Congo.

OPEC ta kara da cewa ta hanyar ci gaba da ƙarfin da ta samu a watan Fabrairu, Nijeriya ta zarce Algeria, wacce ta samar da ganga 909,000 a kowace rana, da kuma Congo, wacce ta samar da ganga 263,000 a kowace rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here