Mutane biyu daga Kano sun mutu a wajen haƙar ma’adanai

0
171

Wasu ƴan asalin jihar Kano su biyu sun rasa rayukansu a wajen haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, dake yankin Farin Doki na karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 8 na safiyar ranar Lahadin data gabata.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce mutanen sun gamu da ajalin su yayin da suke haƙar ma’adinan.

Jami’an yan sanda daga ofishin Erena tare da taimakon mazauna yankin sun kai ɗauki, amma an samu mutanen sun rasu kafin ceto su, sanadiyar ruftawar da dutse yayi akansu suna tsaka da aikin haƙar ma’adanai.

Tuni dai an kai gawarwakin su zuwa asibitin Zumba dake jihar ta Neja.

Rundunar ‘yansandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta ja kunnen jama’a da su guji irin wannan aiki da ya ke barazana ga rayuka, tsaro da tattalin arziƙin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here