Kungiyar Samarin Tijjaniya ta kasa tace bata goyon bayan Hukuncin da kotun ECOWAS ta yanke akan masu yin ɓatanci ga Annabi muhammadu SAW.
Tun da farko ECOWAS ta nemi gwamnatin Kano ta soke dokar yin hukunci mai tsauri akan duk wanda aka samu da laifin cin zarafin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW, sai dai gwamnatin Kano tayi watsi da hakan inda tace duk wanda yayi ɓatanci zai fuskanci matsanancin hukunci.
A wata sanarwa da Kungiyar ta fitar Mai dauke da sanya hannun Babban Sakataren ta Shehu Tasi’u Ishaq da sakataren yada labaran ta Abubakar Balarabe Kofar Na’isa Kungiyar tayi tir da Allah wadai da matakin ECOWAS.
Kungiyar tace yin hakan ya sabawa dokokin addinin musulunci, Wanda kuma duk wani Hukuncin da zai ci Karo da dokokin Ubangiji ba zasu goyi bayansa ba.
Daga nan kungiyar Samarin Tijjaniyya ta kasa tayi kira ga Gwamnati a kowane mataki da lallai a tabbatar da bin dokokin da suka tabbatar da tsarin addinin musulunci akan duk Wanda ya keta alfarmar fiyayyen halitta kamar yadda yake a kundin dokokin shari’ar Musulunci.
Kungiyar kuma ta yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa yadda ta jaddada matsayinta na tabbatar da dokokin da suka shafi hukunta duk Wanda yayi batanci ga Janibin Annabi muhammadu SAW.