Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje CON, ya yi ganawa ta musamman da wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP daga Kano.
Wadanda aka yi ganawar da su sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Sulaimaiman Abdurrahman Kawu sumaila da dan majalisar tarayya mai.wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Dala Hon. Ali Madaki da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta Makoda Hon. Badamasi Ayuba.
Wasu na kallon haka a matsayin wani yunkuri na ko zasu koma APC.
Hakan na kunshe cikin wani sako da Aminu Dahiru mataimaki na Musamman ga Ganduje ya wallafa a Shafinsa na Facebook.