Shugaban ƙasa Tinubu ya kaddamar da cigaban aikin sashi na biyu a aikin titin Abuja, Kaduna zuwa Kano, a ranar Lahadi data gabata.
Shugaban ƙasar ya samu wakilcin gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, inda yace babban burin sa shine kammala faɗaɗa ɗaukacin manyan titunan dake faɗin Najeriya don sauƙaƙa zirga-zirga ga yan ƙasa.
Yace hanyar Abuja zuwa Kano nada muhimmanci wajen haɗa yankin arewa da kudu, sannan gwamnatin tarayya tana son tallafawa yanayin sufurin al’umma.
Tinubu ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta gaji ayyukan da tsohuwar gwamnati ta fara bata kai ga kammalawa ba, wanda kuma a yanzu gwamnatin sa ke kokarin gamawa.
A nasa jawabin ministan ayyuka David Umahi, ya yabawa kokarin Tinubu dangane da aikin titin.